18 Disamba 2025 - 21:38
Source: ABNA24
An Gudanar Da Bikin Buɗe Babban Littafi Na "Runbun Ilimin Shi'a" 

A wani biki da aka gudanar a yau, Alhamis, 18 ga Disamba, 2025, a zauren taro na Majalisar Duniya ta Ahlul Bayt (AS) da ke Qom, an bayyana "Ƙwafi Runbun Ilimin Shi'a".

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: An gudanar da bikin buɗe "Ƙwafi na littafin Runbun Ilimin Shi'a" mai taken "Gabatar da Shi'a a Duniyar Yau; Bukatu da Kalubale" a yau, Alhamis, 18 ga Disamba, 2025 a zauren taro na Majalisar Duniya ta Ahlul Bayt (AS).

A cikin wannan biki, Ayatullah Ramezani, babban sakataren Majalisar Duniya ta Ahlul Baiti (AS), Hujjatul Islam Wal Muslimin Dr. Mohammad Taqi Subhani, shugaban Mu'assatul Bayan Littawaasil Wat-Ta'asil, Hujjatul Islam Wal Muslimin Dr. Ahmad Waezi, shugaban ofishin yada sakunan Musulunci, Hujjatul Islam Wal-Muslimin, Dr Muhsin Weri Daraktan Sashen Tarihi na Jami'ar Bakiril Uloom (AS), Hujjatul Islam Wal-Muslimin Sayyid Kalab Jawad Naqvi, babban sakataren majalisar malamai ta Indiya, da Dr. Mohammad Ali Rabbani, babban daraktan hadin gwiwar kimiyya da ilimi na kungiyar al'adun Musulunci da sadarwa, sun gabatar da jawabai. A cikin wannan taro, Ayatullah Ramezani ya bayyana hankali da tunani a matsayin tushe na asali a cikin bincike ya ce: Idan kuka duba tarin ayoyin kur’ani mai tsarki, za ku ga cewa ayoyi kusan dari uku ne suna karfafa batun yin hankali da tunani; wannan batu ne mai matukar muhimmanci. Allah yana cewa a cikin aya ta goma ta Suratul Anbiya: «لَقَدْ أَنزَلْنَا إِلَیْکُمْ کِتَابًا فِیهِ ذِکْرُکُمْ أَفَلَا تَعْقِلُونَ».

“Hakika mun saukar muku da littafi wanda ambatonku ya ke cikinsa Shin ba za ku yi hankali ba?” Wani lokaci ana iya tunatar da mu cewa ne yasa ba a yin amfani da wannan matakin tunani da hankali a cikin al'ummomin Shi'a da Musulunci ko a tsakanin bil'adama ba? Wannan shine dalilin da ya sa marigayi Kulayni (Allah Ya yarda da shi) ya sanya wa babinsa na farko a cikin littafin Al-Kafi suna da "Littafin Hankali da Jahilci." Wannan ya kamata ya zama ruhiyyar da ke kan gaba, don haka tattaunawar da muke son gabatarwa ga duniya a ƙarƙashin sunan Shi'anci ya kamata ta kasance bisa ga kafa hujja.

Your Comment

You are replying to: .
captcha